Steven Pienaar zai yi jinyar watanni shida

Steven Pienaar Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Steven Pienaar

Dan kwallon Tottenham Hotspur Steven Pienaar ba za a fara buga kwallo dashi ba a gasar premier ta Ingila a kakar wasa ta bana saboda rauni.

A don haka, dan wasan na Afrika ta Kudu zai shafe watanni shida yana jinya.

Pienaar ya takawa Spurs kwallo a wasanni 11 a kakar wasan data wuce kuma yaji rauni a wasansu da Athletic Bilbao na sada zumunci.

Dan kwallon mai shekaru 29 ya koma Tottenham ne daga Everton a watan Junairun 2011 akan fan miliyon biyu da rabi.