Ameobi ya sabunta kwangilarsa a Newcastle

shola Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Shola Ameobi

Dan kwallon Newcastle United Shola Ameobi ya sabunta kwangilarsa na karin shekaru biyu don cigaba da taka leda a St James' Park.

Dan wasan mai shekaru 29 wanda yake tare da kulob din tun yana dan shekara 13, ya zira kwallaye tara a gasar premier a kakar wasan data wuce.

Ameobi ya ce"Newcastle ne kulob dina a koda yaushe kuma ina jiran cigaba da buga kwallo na karin shekaru uku masu zuwa".

Kocin Newcastle Alan Pardew yace "Ya yi aiki tukuru anan, kuma yasan dabarar murza leda".

Ameobi ya bugawa Newcastle a wasan farko ne a watan Satumbar 2000 kuma ya takawa kulob din wasanni 300 inda yaci kwallaye 70.