U20: An fitar da Kamaru da Masar

U20: An fitar da Kamaru da Masar Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dama kasashen uku ne daga Afrika su tsallake zuwa zagaye na biyu

Mexico ta fitar da Kamaru a bugun fanareti, yayin da Argentina ta doke Masar da ci 2-1 a zagaye na biyu na gasar cin kofin duniya ta 'yan kasa da shekaru 20 a Colombia.

Kamaru ta fita ne bayan da ta tashi 1-1 a wasan da ta kara da Mexico ranar Talata.

Kamaru ta zubar da fanareti uku yayin da Mexico ta cinye duka na ta ukun.

Kocin Kamaru Martin Ndtoungou Mpille ya ce rashin maida hankali ne ya janyo aka farke kwallon da suka fara zirawa.

"Babu wani karin bayani kan fanaretin da muka zubar," a cewarsa.

Ita ma Masar ta fita bayan da ta sha kashi da ci 2-1 a hanun Argentina - duka kwallaye ukun an zira su ta bugun fanareti.

Bayan wasan 'yan wasan Masar sun yi korafin cewa fanaretin farko na Argentina bai halarta ba. Amma daga baya kocinsu El Sayed Diaa ya yi watsi da batun.

"Haka kwallon kafa ta gada, ba mamaki an samu kuskure, ba mamaki kuma ba a samu ba," a cewarsa.