Dage gasar premier ba zai yi dadi ba-Ecclestone

ecclestone
Image caption Bernie Ecclestone

Mai kungiyar Queens Park Rangers-QPR Bernie Ecclestone yace za a samu sako mara dadi idan har aka dage wasu wasannin gasar premier saboda tarzoma a Ingila.

A ranar Alhamis ne za a yanke shawara ko za a dakatar da wasu wasanni uku da ya kamata a buga a London a karshen mako.

QPR zata kara da Bolton a filin Loftus Road a ranar Asabar kuma Ecclestone nada kwarin gwiwar cewa za a buga wasan.

Ya shaidawa BBC cewar"Sako ne mara dadi ga duniya, idan har aka fasa buga wasannin".

Wannan tashin hankalin dai ya janyo an dage wasu wasanni sada zumunci hadda na Ingila da Holland da kuma na Najeriya da Ghana, amma kuma Ecclestone ya bayyana batun a matsayin 'annoba'.