Tarzomar London: Babu tabbas kan fara gasar Premier

Tarzomar London: Babu tabbas kan fara gasar Premier
Image caption A ranar Asabar ne aka shirya fara gasar Premier

Hukumar kula da gasar Premier a Ingila za ta yanke hukunci ranar Alhamis kan ko za a dage wasannin farko na gasar saboda tarzomar da ake fama da ita a kasar.

Ana ta samun tarzoma a kasar tun ranar Asabar, abin da yake neman fin karfin 'yan sanda.

Wata sanarwa ta hadin gwiwa daga Hukumar ta Premier da kuma Hukumar League ta ce: "Muna tattaunawa da kulob-kulob na Ingila, da 'yan sanda da kuma hukumomi.

"Za a fitar da wata sanarwar nan gaba bayan an sake nazari kan halin da ake ciki ranar Alhamis."

Wasanni uku aka shirya gudanarwa a London ranar Asabar, duka da karfe uku agogon GMT: Tottenham da Everton, Fulham da Aston Villa da kuma QPR da Bolton.

Sanarwar ta ranar Talata ta bayyana cewa babu wani dalili da zai sa ayi tunanin dage wani wasa da za a yi a wajen London", amma an bayar da ita ne kafin tarzomar ta bazu zuwa West Midlands da Manchester.

West Bromwich za ta karbi bakuncin Manchester United ranar lahadi da yamma kafin Manchester City ta kara da a gida da Swansea ranar Litinin da daddare.

Tarzomar dai ta hana a gudanar da wasannin sada zumunci tsakanin Ingila da Holland wanda aka shirya yi ranar Laraba a London, da kuma na Najeriya da Ghana wanda da za a yi a Watford ranar Talata.

An kuma dage wasannin Carling Cup da aka shirya yi a Charlton, West Ham, Crystal Palace da Bristol City.