Ba za mu bari a sake tarzoma ba - Cameron

David Cameron Hakkin mallakar hoto BBC News 24
Image caption Cameron ya ce za a hukunta duk mai hannu a lamarin

Fira ministan Birtaniya David Cameron ya fada ma majalisar dokokin kasar cewa gawmnatinsa ba za ta kyale a sake yin tarzoma da sace kayan mutane a kasar ba.

An shafe dare hudu ana tarzoma a birnin London - wacce kuma daga bisani ta bazu a zuwa wasu biranen kasar.

Gungun matasa sun rinka fasa shaguna suna sata da kona motoci da kuma gidajen jama'a.

Ya ce babu wani dalili na yin tarzomar ga gungun matasan da ke jiran irin wannan dama.

Mr Cameron ya dora alhakin wannan al'ammari, ba wai a kan talauci ba, a'a a kan yanayin da yara suke girma a ciki.

"Galibin yara ba sa iya bambanta abun da ya dace da wanda bai dace ba.

Baki ya zo daya

Shi ma jagoran 'yan adawa Eid Miliband ya yi Allah wadai da lamarin da ya afku, sannan ya nemi da a kara daukar matakai domin kawo karshen lamarin.

Duka dai mambobin Majalisar bakinsu ya zo daya, wajen watsi da tarzomar da aka yi a wasu sassan Burtaniyar.

A halin da ake ciki kuma, 'yan sanda a Ingila sun kai samame a kan gidaje da dama don cafke mutanen da ake zargi da hannu a tarzoma da kwasar ganimar da aka yi.

A wasu wuraren ma 'yan sandan na kame mutanen ne tare da kwace wasu kayayyakin da suka sata.

A yanzu kotuna na aiki tukuru - har cikin dare domin hukunta wadanda ke da hannu a lamarin.

Karin bayani