Fabregas da Nasri na gabda barin Arsenal

Fabregas da Nasri Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Fabregas da Nasri

'Yan kwallon Arsenal na tsakiya Cesc Fabregas da Samir Nasri duk suna gabda kamalla yarjejeniyar barin kulob din.

Fabregas na kan hanyarsa ta sanya hannu don taka leda tare da zakarun Turai Barcelona akan kusan fan miliyon 35.

Shi kuma Nasri zai koma Manchester City ne akan kwangilar kusan fan miliyon 22 zuwa 24.

Wata majiya daga wajen babban jami'i a Arsenal, ya nuna cewar kudin da aka samu wajen sayarda Fabregas za a kashe ne wajen siyo sabbin 'yan kwallo.

A halin yanzu dai ana alakanta Gunners din da sayen Scott Dann, Phil Jagielka da kuma Gary Cahill.

Idan har Fabregas ya bugawa Arsenal wasanta na neman gurbin zuwa gasar cin kofin zakarun Turai tsakaninta da Udinese, to ba zai yiwu ya bugawa Barcelona ba a gasar zakarun Turai.