Dan Kamaru Emana ya koma Al Hilal a Saudiya

Achille Emana Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Achille Emana

Dan kwallon Kamaru Achille Emana ya kulla yarjejeniyar shekaru hudu tare da kungiyar Al Hilal ta Saudi Arabia.

Dan wasan mai shekaru 29 ya bar kungiyar Real Betis ne don komawa taka leda a Saudi Arabia akan dala miliyon shida.

Ana saran Emana zai isa birnin Riyadh a ranar Lahadi don hadewa da sauran tawagar Al Hilal.

A shekaru uku daya taka leda a Betis,Emana ya zira kwallaye 34 a wasanni 91.

Dan kwallon a baya ya taka leda tare da Valencia a Spain da kuma Toulous a Faransa.

Emana ya kasance dan Afrika na uku daya koma kungiyar Al Hilal kafin a fara kakar wasa ta bana.