Colombia 2011: Najeriya ta doke Ingila

Colombia 2011: Najeriya ta doke Ingila Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Flying Eagles sun lashe duka wasanni hudun da suka yi

Kwallon da Edafe Egbedi ya zira a zagaye na biyu ta baiwa Najeriya damar doke Ingila da ci 1-0, inda ta kai zagayen daf da na kusa da na karshe a gasar cin kofin duniya ta 'yan kasa da shekaru 20.

A yanzu Najeriya, wacce ta taba kaiwa zagayen karshe a shekarun 1989 da 2005, za ta kara da Faransa ranar Lahadi mai zuwa.

"Wasa ne mai tsauri, amma mu muka fi kowa shiga cikin hadari," a cewar kocin Najeriya John Obuh.

Matthew Phillips ya samu damar ramawa Ingila har sau biyu amma ya baras da damar.

Fiye da 'yan wasan Ingila 30 ne kulob-lukansu ba su basu damar taka leda a gasar ba.

"Idan ka kalli sakamakon wasan, za ka iya cewa gazawa ce," a cewar kocin Ingila Brian Eastick.

"Hanya daya tilo ta sauya wannan ita ce ta samar da dokokin da za su sa kulob-kulob su dinga sakin 'yan wasansu."