An dage wasan Tottenham da Everton

london
Image caption Tashin hankali ne ya tilasta dage wasan Spurs da Everton

An dage wasan gasar premier ta Ingila tsakanin Tottenham da Everton wanda ya kamata su buga a ranar Asabar saboda zanga zangar da ake yi a London.

A karshen makon daya gabata ne aka samu tashin hankali a Tottenham sannan ya bazu a wasu manyan birannen Ingila.

Shugaban gasar Premier Richard Scundamore ya ce babu tantama za a buga sauran wasanni tara na gasar.

Shi dai Firayi Ministan Birtaniya David Cameron ya bada shawarar a buga wasanin da wuri kafin lokacin da a baya aka tsara saboda taimakawa 'yan sanda wajen tabbatar da tsaro.

Amma dai hukumar dake kula da gasar ta Premier ta ce ba za a canza lokacin karawar ba.