Liverpool ta sayi Enrique daga Newcastle

Jose Enrique
Image caption Jose Enrique shi ne biyar da Liverpool ta saya a bana

Liverpool ta kammala sayen dan wasan baya na Newcastle Jose Enrique kan farashin da rahotanni suka ce ya kai fan miliyan shida.

Dan wasan mai shekaru 25 ya zamo na biyar da koci Kenny Dalglish ya saya a bana.

"Wannan na daya daga cikin ranakun da nafi kowanne farin ciki a rayuwata. Na zo daya daga cikin manyan kulob bawai kawai a Ingila ba, harma a duniya," a cewar Enrique wanda dan kasar Spain.

Enrique zai hadu da Jordan Henderson, Charlie Adam, Alexander Doni da Stewart Downing wadanda duk suka koma Liverpool a bana.

Liverpool ta kashe makudan kudade a kan Andy Carroll da Luis Suarez a watan Janairu, kuma yanzu ma sun kara kashe kudaden kan wasu 'yan wasa.