West Brom ta yi watsi da tayin Wigan kan Osaze

Osaze Odemwingie Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Osaze Odemwingie ya taka rawar gani sosai a kakar bara

West Brom ta yi watsi da tayin da Wigan ta mika mata na sayan dan wasan gaban Najeriya Peter Osaze Odemwingie.

Dan wasan mai shekaru 29 shi yafi kowa zira kwallaye a West Brom - inda ya zira kwallaye 15 goals a kakar farko da ya buga a Premier.

Rawar da ya taka ta janyo masa farin jini a wajen sauran kulob-luka a Ingila.

Sai dai Daraktan kwallo a West Brom Dan Ashworth ya ce suna yin duk mai yiwuwa wajen rike Odemwingie wanda saura shekara biyu kwantiraginsa ta kare.

"Mun yanke shawarar rike manyan 'yan wasanmu bana - kamar Peter Osaze da kuma kara sayen wasu kwararrun 'yan wasan," a cewar Ashworth.

"Peter yana jin dadin zamansa anan kuma magoya bayanmu suna kaunarsa, kuma shi ma yana jin dadin zama da su.