U 20:An fidda Argentina da Columbia

argentina Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tawagar 'yan kwallon Argentina

Mexico da Portugal sun tsallake zuwa zagayen kusada a gasar cin kofin duniya ta matasa 'yan kasada shekaru 20 sakamakon nasarar da suka yi a zagayen gabda na kusada karshe.

Mexico ta samu gurbinne bayan ta casa mai masaukin baki wato Columbia da ci uku da daya a wasan da suka ranar Asabar.

Ita kuwa Portugal ta fidda Argentina ne a gasar bayan data doke Argentinar daci biyar da hudu a bugun fenariti.

Tunda farko Portugal da Argentina sun buga wasa na tsawon minti 120 amma babu ci.

A ranar Lahadi za a samu karin kasashe biyu da zasu tsallake zuwa zagayen kusada karshe.

Zakarun Afrika wato Najeriya zasu kara da zakarun nahiyar Turai wato Faransa.

Sai kuma Brazil wacce zata kece raini da Spain.