Da Silva zai yi jinyar makwanni goma

Rafael da Silva Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Rafael da Silva

Dan kwallon Manchester United Rafael da Silva zai shafe makwanni goma yana jinya saboda targade a kafadarshi.

Dan wasan mai shekaru 21 ya ji ciwo ne a lokacin horo kafin wasan United da West Brom.

Rafael ya bugawa United wasanni 73 tun zuwansa a shekara ta 2008.

Baya ga shi Patrice Evra da Antonio Valencia da Michael Owen da kuma Javier Hernandez duk suma suna da rauni.

Amma dai a cewar kocin United Sir Alex Ferguson dan wasan Mexico Hernandez ya komo horo bayan rashin lafiyar da yayi.