Cesc Fabregas ya koma Barcelona

Cesc Fabregas
Image caption Cesc Fabregas ya taka rawar gani sosai a Arsenal

Barcelona ta kammala cinikin Cesc Fabregas daga Arsenal bayan da ya rattaba hannu a kan kwantragin shekaru biyar da kungiyar.

Tsohon kyaftin din na Arsenal mai shekaru 24 ya bayyana ne a gaban magoya bayan kungiyar Barcelona su sama da dubu talatin a babban filin wasa na Nou Camp bayan tantancewar likita a ranar Litini.

Kungiyar Arsenal dai za ta karbi fan milyan 30 a kan dan wasan, sa'annan fan miliyan biyar zai biyo baya a sakamakon yawan wassanni da kofuna da kungiyar za ta lashe nan gaba.

Fabregas ya bar kungiyar Barcelona ne a shekarar 2003 lokacin yana dan shekara 16 da haihuwa.

A yanzu dai ya sake dawowa kugiyar kuma zai sanya rigar wasa ce mai namba 4, wato tsohuwar rigar da mai horar da kungiyar Pep Guadiyola ya sanya lokacin yana dan wasa a Barcelona.

Shafin intanet na Barcelon dai ya bayyana cewar Cesc Fabregas ya gama gwajin lafiya ba tare da wata matsala ba.

Likitan kungiyar Richard Pruma, ya kara da cewar ya amince da gwajin kuma Fabregas na iya fara wasa ba tare da bata lokaci ba.