Colombia 2011: Faransa ta fitar da Najeriya

Colombia 2011: Faransa ta fitar da Najeriya
Image caption Kocin Flying Eagles na Najeriya John Obuh

Faransa ta doke Najeriya da ci 3-2 a wasan dab da na kusa da na karshe na gasar cin kofin duniya ta 'yan kasa da shekaru 20 a kasar Colombia.

An tashi 1-1 ne bayan kammala minti 90 na farko.

Daga nan ne kuma aka tafi karin lokaci na minti 30, inda a 15 din farko Faransa ta zira kwallaye biyu.

Wannan nasara dai ta baiwa kasar ta Faransa damar tsallakewa zuwa wasan kusa da na karshe a karon farko a tarihinta.

Hakazalika kuma ta kawo karshen fatan da Najeriya ke da shi - wacce ta kasance kasar Afrika daya tilo da ta rage a gasar.