An sace mahaifin John Obi Mikel

Mikel Obi
Image caption Mikel ya taka leda a wasan da Chelsea ta buga ranar Lahadi

Rahotanni sun ce wasu da ba a sa ko su wanene ba sun yi awangaba da mahaifin dan wasan Chelsea da Najeriya John Obi Mikel.

Tun ranar Juma'a ne dai aka nemi mahaifin John Obi Mikel din aka rasa.

Kamfanin da ke wakiltar dan wasan Sport Entertainment & Media Group, sun bayyana cewa an sanar da dan wasan halin da mahaifin na sa ya samu kansa a ciki.

Sanarwar da kamfanin ta bayar ta kara da cewa: "Kawo yanzu ba a gabatar da wata bukatar neman kudin fansa ba,"

"Amma Mikel ya yanke shawarar taka leda a wasan da Chelsea ta kara da Stoke City ranar Lahadi domin taimakawa kulob din na sa".

Wannan ba shi ne karo na farko da aka yi garkuwa da dangin dan wasan da ke taka leda a Premier ta Ingila a Najeriya ba.

A shekara ta 2008 ma an yi garkuwa da dan uwan tsohon dan wasan Everton Joseph Yobo.