Chelsea na taka tsan-tsan akan Modric

modric Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Luka Modric

Shugaban Chelsea Bruce Buck ya ce babu tabbas ko kulob din zai kara bada tayi akan dan wasan Tottenham Luka Modric.

Kocin Blues Andre Villas-Boas ya bayyana cewar suna karancin dan kwallon tsakiya sakamakon tashi babu ci da suka yi tsakaninsu da Stoke a ranar Lahadi.

Bayanda Spurs taki amincewa da tayin pan miliyon 27 akan Modric, akwai tantama ko Chelsea zata kara bada tayin dan wasan kafin 31 ga watan Agusta.

Buck yace"Spurs taki amincewa da tayinmu kuma watakila ba kara tayashi ba".

Tottenham na jan kafa wajen sayarda Modric mai shekaru 25.

A yanzu dai a tsakiyar Chelsea akwai 'yan kwallo hudu wato John Obi Mikel da Ramires da Frank Lampard da kuma Josh McEachran a yayinda shi kuma Michael Essien ke jinya.