Ferdinand daVidic da Silva za su yi jinya

ferdinand
Image caption Rio Ferdinand

Manchester United na fuskantar matsalar 'yan kwallo uku masu rauni wato Rio Ferdinand, Nemanja Vidic da kuma Rafael da Silva.

Ferdinand zai shafe makwanni shida yana jinya sakamakon raunin da yaji a ranar Lahadi a wasan United da West Brom.

Vidic kuma zai jinyar makwanni biyu saboda ciwon kafa.

Rafael kuwa zai jinyar makwanni goma saboda targade a kafadarsa.

Ciwon Ferdinand na nufin cewar sai a watan Oktoba zai komo taka leda, kenan ba zai bugawa Ingila wasanta da Bulgaria da kuma na Wales.