Aguero ya yi kama da Romario - Mancini

Sergio Aguero
Image caption Fan miliyan 38 City ta sayi Sergio Aguero da Athletico Madrid

Kocin Manchester City Roberto Mancini ya kamanta Sergio Aguero da tsohon dan wasan Brazil Romario bayan rawar da ya taka a wasansu da Swansea.

Dan wasan wanda City ta saya a kan fan miliyan 38, ya zira kwallaye biyu sannan ya taimaka aka ci daya a wasan da suka lallasa Swansea da ci 4-0.

Romario wanda ya lashe gasar cin kofin duniya da Brazil a 1994, ya zira kusan kwallaye 1,000 a rayuwar tamolarsa.

"Sergio kamar Romario ya ke, daidai suke," a cewar Mancini wanda ke cike da farin ciki.

"Duk da cewa bai gama cika dari-bisa-dari ba, amma zai taka leda sosai."

Aguero ya shigo wasan ne bayan an dawo hutun rabin lokaci, lokacin da City ke kan gaba da ci 1-0.

Amma nan take sai ya nuna kansa, inda ya zira kwallaye biyu, sannan ya taimaka aka ci daya, baya ga haskakawar da ya rinka yi har zuwa karshen wasan.