An dakatar da Gervinho na wasanni uku

gervinho Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Gervinho ya cukeme Barton

An dakatar da dan kwallon Arsenal Gervinho na wasanni uku saboda kararsa da aka yi a wasansu da Newcastle na gasar premier ta Ingila.

Dan wasan mai shekaru 24 an kore shine a wasan bayan fadan da yayi da Joey Barton inda dan kwallon Newcastle din ya fadi kasa.

Gunners ta daukaka kara akan dakatarwar wasanni uku din, inda ta ce hukuncin yayi tsauri.

Amma hukumar dake kula da kwallon Ingila ta yi watsi da bukatar Arsenal wato kenan dakatar da dan Ivory Coast din zai soma aiki take.

Gervinho mai shekaru 24 ya koma Arsenal ne daga Lille akan fan miliyon 10 da rabi, kuma ba zai buga wasansu da Liverpoop da Manchester United da kuma Swansea.

Sannan kuma da Arsenal da Newcastle ana tuhumarsu da kasa hana 'yan kwallonsu shiga yamusti, a yayinda Alex Song na Gunners yake fuskantar tuhuma ta daban saboda haurin Barton.