Uefa za ta binciki kwangilar Man City da Etihad

ciity Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Filin wasan Manchester City

Shugaban kwamitin dake kula da ka'idar kashe kudi na Uefa Jean-Luc Dehaene ya ce zai sake nazarin yarjejeniyar Manchester City tsakaninta da kamfanin Etihad mai daukar nauyin kulob din.

Yarjejeniyar shekaru goma takai kusan fan miliyon dari hudu, inda kulob din zai amfani da sunan Etihad a jikin rigar kwallo da kuma filin wasa.

Amma da yake City da Etihad duk suna kusan yanki daya ne a Abu Dhabi, masu suka na kallon lamarin a matsayin wata dabarar saba ka'idar dokar kashe kudi na Uefa.

Koda yake City bata maida martani ma, amma ta ce kudaden da aka bayyana ba dai dai suke ba.

Shugaban kwamitin Jean-Luc Dehaene ya ce akwai tambaya akan yarjejeniyar.

Manchester City tun a shekara ta 2008 da Sheikh Mansour bin Zayed Al Nahyan ya sayi kulob din ta kashe makudan kudade ba tare cin riba ba.