Federer ya yi galaba akan del Potro

Hakkin mallakar hoto BBC World Service
Image caption Roger Federer

Roger Federer ya kai zagaye na uku a gasar Tennis ta Western & Southern Open a Cincinati a Amurka bayan ya yi galaba akan Juan Martin del Potro.

Federer wanda shine na uku a fagen Tennis a duniya ya sha kashi ne a hannu del Potro a wasan karshe da suka buga a shekarar 2009 a gasar US Open.

Federer dai ya lashe gasar ne da maki 6-3 7-5 a Cincinati.

A bangaren mata, Serena Williams ce ta doke Maria Sharapova, inda ta kai zagayen na uku.