Ghana za ta buga wasan sada zumunci da Brazil

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ghana ta sha kashi ne a hannu Brazil da ci daya da nema a Sweden a shekarar 2007

Ghana zata buga wasan sada zumunci da Brazil a ranar 5 ga watan Satumba a birnin Landan.

Hukumar kwallon Ghana ce ta bayyana hakan a shafin ta na Intanet a ranar Laraba.

Za'a a buga wasan ne, kwanaki uku bayan da Ghana ta kara da Swaziland a birnin Accra a wasan share fage na taka leda gasar cin kofin Afrika da za'a buga a shekarar 2012.

Za'a buga wasan ne kuma a filin wasa na Craven Cottage inda kungiyar Fulham ke taka leda.

Kasashen biyu sunyi karawa ta karshe ne a karshen shekara ta 2007 a kasar Sweden, inda Brazil ta yi nasara da ci daya mai ban haushi.