Ba za'a fara gasar laliga ba a karshen mako

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan wasan Barcelona, Pedro

Za'a fuskanci jinkiri wajen fara kakar wasanni ta bana a gasar laliga ta Spaniya bayan kungiyar 'yan wasa da Hukumar shirya gasar su ka gaggara cimma yarjejeniya kan wasu kudade.

'Yan wasan dai suna so a basu tabbacin za'a rika biyan su albashi ako wani wata, koda ma, kungiyarsu na fuskantar matsalar durkushewa, ko kuma su shiga yajin aiki.

A yanzu haka dai manyan kungiyoyi shida a gasar ta laliga na fuskantar durkushewa.

Kungiyoyi da dama ne dai a Spaniya basa biyan albashi 'yan wasansu akan kari abun da kuma ya sanya 'yan wasan ke binsu bashin albashi na wasu watanni da dama.