Manchester City na gab da sayan Nasri

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Samir Nasri

Kungiyar Manchester City na gab da cimma yarjejeniyar sayan Samir Nasri daga Arsenal.

Rahotani na nuni da cewa kungiyar City za ta sayi dan wasan daga Arsenal ne akan fam miliyan 25.

Nasri, dai ya koma Arsenal ne daga kungiyar Marseille a shekarar 2008, kuma a yanzu haka saura watanni 12 kwantaragin dan wasan ya kare da Arsenal.

Nasri zai zama babban dan wasa na biyu da zai bar Arsenal a wannan makon bayan da Cesc Fabregas ya koma Barcelona a ranar Litinin.