Ba ni da niyyar barin Wes Brom - Osaze

Image caption Osaze Odemwingie

Dan wasan Najeriya wanda ke taka leda a kungiyar Wes Brom ta Ingila Osaze Odemwingie ya musanta rahotannin dake nuni da cewa yana kokarin barin kungiyar.

Odemwingie a wata sanarwa da ya buga a shafinsa na Twitter ya kara ba magoya bayan kungiyar hakuri game da rashin sabonta kwantaraginsa da bai yi ba har yanzu.

Ana dai zargin Osaze ne da kin sabonta kwantaraginsa, domin yana jiran tayi mai tsoka daga wata kungiya.

Osaze dai ya ce yana kara tattaunawa ne da kungiyar ta Wes Brom kan wa'adin kwantaraginsa, kafin su cimma yarjejeniya.