Tottenham na tattaunawa da Adebayor

Emmanuel Adebayor.
Image caption Adebayor ya dade yana neman makoma

Manajan kungiyar Tottenham Harry Redknapp ya bayyana cewa suna tattaunawa da Manchester City kan karbar aron dan kasar Togo Emmanuel Adebayor.

Adebayor dai ya dan sami rashin jituwa da Roberto Mancini a shekarar da ta gabata, wanda hakan ya kai ga bada aron sa ga kungiyar Real Madrid ta kasar Spaniya.

Tottenham da Manchester City dai sun dauki tsawon lokaci suna tattaunawa kan bada aron dan wasan, Adebayor dai na neman a abiya shi fan 170,000 a sati wanda hakan ke neman zama matsala a tsakanin kungiyoyin.

Harry Redknapp ya kuma bayyana cewa shugaban kungiyar su na kan tattaunawa da Man City don samun maslaha.

Emmanuel Adebayor dai ya bar kungiyar Arsenal ne zuwa Manchester City a kan fan miliyan 25 a 'yan shekarun da suka gabata.

Kocin Man City Roberto Mancini ya jaddada cewa Adebayor ba shi da abin da zai tabuka a Manchester City.

Adebayor dai ya zura kwalaye biyu a ragar Tottenham a wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin zakarun Turai da aka kafsa a filin wasa na Bernabeu na Real Madrid.

A baya dai magoya bayan Tottenham sun yita masa wake suna masa zinde a wasannin da suka kafsa da Real Madrid, amma dan wasan ya ce ya ganin a wanan karon waken zai sauya.

A yanzu dai Tottenham na matukar neman dan wasan gaba bayan da suka sayar da Robbie Keane ga kungiyar LA Galaxy ta kasar Amurka.