Petr Cech zai yi jinya na makwanni hudu

Image caption Petr Cech

Mai tsaron gidan Chelsea Petr Cech zai yi jinya na tsawon makwanni hudu, bayan raunin da ya samu a gwiwarsa a lokacin da yake horo.

Cech, mai shekarun haihuwa 29, ba zai samu buga wasannin da Chelsea za ta buga da Wes Brom da Norwich da Sunderland da kuma Manchester United ba.

Kocin Chelsea Andre Villas-Boas zai zabi tsakanin Hilario ko kuma Ross Turnbull, domin maye gurbin Cech, kafin ya murmure.

"Cech ya fadi ne akan kafarsa, kuma ba wani horo mai tsauri yake yi ba a lokacin," In ji Villas-Boas.

Raunin da Cech ya samu yasa ba zai samu damar bugawa ba a wasan da kasarsa ta Jamhuriyar Czech za ta buga da Scotlanda a wasan share fage na gasar cin kofin Turai da za'a buga a shekarar 2012.