Chelsea ta cimma yarjejeniya kan Romelu Lukaku

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Romelu Lukaku

Chelsea ta cimma yarjejeniya da kungiyar Anderlecht na sayan dan wasan gabanta Romelu Lukaku.

Kungiyoyin biyu sun amince ne akan kudi fam miliyan 20.

Akwai yiwuwar dan wasan mai shekarun haihuwa 18 ya taka leda a wasan da Chelsea za ta buga da West Brom a ranar asabar.

"Nayi mafarkin takawa Chelsea leda tun ina shekara 10, dama ce ta samu." In ji Lukaku

Lukaku dai ya yi fice ne a Belgium bayan ya zama dan wasan da yafi zura kwallo a kakar wasa ta shekarar 2009-2010, a lokacin yana shekara 16.

Dan wasan ya zura kwallaye 16 a wasanni 37 da ya buga a kakar wasan bara, kuma ya zura kwallon farko wa kasarshi ta Belgium a wasan da ta doke Rasha da ci biyu da nema a watan Nuwamban bara.