Everton na fuskantar matsalar sayan 'yan wasa

Hakkin mallakar hoto PA

Everton na fuskantar matsalar sayan 'yan wasa a kakar wasan bana, saboda sun gaggara aron kudi daga banki.

Shugaban kungiyar Bill Kenwright ya ce kungiyar na fuskantar matsala ne da banki.

Babu dai dan wasan da kungiyar ta saya a bana, abun da kuma yasa suke fuskantar matsin lamba daga magoya bayan ta.

"Mun kai wani mataki da bankin mu da ba za mu iya aron kudi kuma ba." In ji Kenwright.

Kenwright ya kara da cewa "A gaskiya ana fuskantar matsalar tattalin arziki a duniya, ban san sanar da bata shiga matsala ba, har da kwallon fa. Attajirai na kawai abun be shafe su ba."