Dan Malaysia ya sayi kungiyar QPR

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tony Fernandez

Wani dan kasuwa dan kasar Malaysia Tony Fernandes ya sayi kungiyar Queens Park Rangers da ta samu shiga gasar Premier ta Ingila a bana.

Dan kasuwan mai shekarun haihuwa 47 ya sayi kashi 66 ne na hannu jarin kungiyar daga Flavio Briatore da kuma Bernie Ecclestone.

Fernandes zai yi aiki tare da Iyalan Mittal, wanda suke ci gaba da rike kashi 33 uku cikin dari na hannun jarin kungiyar.