Andy Murray ya kai zagaye na uku a Cincinnati

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Andy Murray

Andy Murray ya koma samun nasara bayan da ya doke David Nalbandian a wasan zagaye na biyu a gasar Tennis ta Western & Southern Open a Cincinnati.

Murray wanda shine na daya a Burtaniya a fagen Tennis ya sha kashi a zagayen farko a gasar Montreal da ya buga a makon daya gabata, amma sai ya dawo da karfinsa inda ya lallasa Nalbandian a wasanni biyu.

A yanzu haka dai zai kara ne da Alex Bogomolov Jr bayan shima ya doke Jo-Wilfried Tsonga.

Rafael Nadal kuma ya doke Julien Beneteau a yayinda Novak Djokovic ya lallasa Ryan Harrison.