Amfani da waka wajen yakar yunwa

Bob Marley
Image caption Save the Children na fatan hakan zai sa jama'a su taimaka

Kungiyar bada agaji ta Save the Children tana karfafawa mutane gwiwar su sauko da sautin daya daga cikin fitattun wakokin Bob Marley, domin yakar yunwa a Somalia.

Kimanin mutane miliyan takwas ne Majalisar Dinkin Duniya ta ce na fama da matsalar abinci a yankin Kusurwar Afrika - inda lamarin ya fi kamari a Somalia.

An dai fitar da wakar ta Bob Marley mai suna 'High Tide or Low Tide' ne musamman hade da wani shirin fim dake bayyana halin da wadanda ke fuskantar bala'in yunwar da ake fuskanta a yankin na gabashin Afurka.

Kuma an yi hakan ne ta yadda mutane za su iya sauko da shirin hade da sauti daga shafin internet na kungiyar agajin ta Save the Children.

Kungiyar ta Save the Children tace, ta zabi wannan wake ne saboda wani acikinta dake cewa:

"Zan zama dan uwa gareku'. Kuma kungiyar ta yi wannan zabi ne saboda dangantar Bob Marley da nahiyar Afrika da kuma sakonnin hadin kai da kuma fata na gari da ke kunshe a cikin wakokinsa.

Steven Sidebotton na kungiyar agajin ta Save the Children ya ce, ganin cewa mutanen da suka shahara suna aikewa juna mashigar wannan sako ya taimaka sosai wajen wannan kokari na jawo hankali ga halin da ake ciki:

Kungiyar ta Save the Children dai tana fatan tara miliyoyin daloli ta wannan hanya, kuma kungiyar tace tana fatan kasashen da suka ci gaba ma za su dau irin wannan mataki.

A shafin Internet na kungiyar agajin ta Save the Children, an sanya wani sako daga uwargidan marigayi Bob Marley, inda tace, "dole ne fa mu hada kai, mu tashi tsaye mu kawo karshen wannan lamari, ta hanyar samar da abinci ga yara kanana domin ceto rayuwarsu.