Manchester United za ta sayarda hanayen jarin ta

Hakkin mallakar hoto Getty

A yayinda kungiyar Manchester United ke fama da dumbi basusuka akanta, kungiyar na yunkurin sayarda wasu bangarorin hanayen jarin ta ga kasar Singapore domin biyan bashin da ake bin ta.

Manchester United dai na fama da bashin fam miliyan dari biyar da goma sha biyar da kuma kudin ruwa na shekara-shekara na fam miliyan 45.

Kididdiga na nuni da cewa hanayen jarin da kungiyar za ta sayar na iya kawo tsakanin fam miliyan 400 zuwa fam miliyan 600 ga kungiyar.

Hakan na iya habbaka hannun jarin kanfanin zuwa mizanin fam biliyan 1.7 hakan kuma na iya rage yanwan kudin da Glazers ta karba bashi a watan Janairu na 2010.