'Ya kamata a ba Wenger goyon baya'- Dien

Image caption David Dean da Arsene Wenger

Tsohon shugban Arsenal, David Dein ya shaidawa BBC cewa dolene magoya bayan kungiyar su baiwa Arsene Wenger goyon baya da kuma daukaka, ko su rasa shi.

Magoya bayan Arsenal dai na ta sukar Wenger ne saboda rashin lashe kofi da kungiyar ba ta yiwa ba na tsawon shekaru shida, da kuma yadda ya sayar da Fabregas.

Da aka tambaye Dien ko Wenger, zai iya barin kungiyar sai ya ce; " Kwarai zai iya barin kungiyar, musamman idan yaga an matsa mishi."

David Dein, ne dai ya dau Arsene Wenger aiki a shekarar 1996.