Ghana da Najeriya za su hadu a Okutoba

Hakkin mallakar hoto Getty

Ghana da Nigeria za su buga wasan sada zumunci a watan Okutuba, bayan da aka soke wasan 9 ga watan Agusta da kasashen biyu ya kamata su buga saboda tarzoma a Ingila.

Kasashen biyu dai za su fafata ne a filin wasa na Vicarage Road, inda kungiyar Watford ke taka leda.

Hukumar kwallon Ghana ce ta bada tabbacin haka a shafinta na intanent, inda tace za'a buga wasan ne ranar 9 ga watan Okutoba.

An dai soke wasan na baya ne da aka shirya, saboda hukumomin tsaro a Ingila sun ce ba za su iya tabbatar da tsaro ba a lokacin wasan.