Wenger ya ce ba zai bar Arsenal ba

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsene Wenger

Arsene Wenger ya nace cewa, ba zai bar Arsenal ba, duk da sukar da ake yi mai bayan kashin da kungiyar ta sha a hannun Liverpool a filin Emirates.

Magoya bayan kungiyar dai sun ta yiwa Wenger da 'yan wasan ihu bayan da Liverpool ta doke Arsenal a laron farko cikin shekaru 11 a gida.

Sai dai duk da ihun da aka yi musu, Wenger ya ce baya fuskantar matsin lamba.

"Babu yadda za'a yi in bar kungiyar zanyi duk mai yiwuwa domin ganin na farfado da kungiyar." In ji Arsene Wenger.

Aaron Ramsey ne ya zura kwallo a ragarsa sannan kuma ana dab da kammala wasan Luis Suarez ya zura ta biyu.