Chelsea da Valencia sun cimma yarjejeniya akan Mata

Image caption Juan Mata

Chelsea ta cimma yarjejeniya da kungiyar Spaniya ta Valencia kan dan wasanta Juan Mata a kan kudi fam miliyan 23.5.

Dan wasan dai ya bayana a shafinsa na Twitter cewa yana kan hanyarsa zuwa Stamford Bridge domin a duba lafiyarsa, kafin an kammala siyan nasa.

Mata ya rubata a Twitter: "Ina kan hanya zuwa Landan domin a duba lafiya ta, kuma zan dawo Valencia domin in bankwana da abokan arzikin da 'yan uwa. Na gode."

Kungiyar Chelsea a nata bangaren ta ce tana tattaunawa da dan wasan kan wasu ka'idoji kafin a duba lafiyarsa.