Volley Ball: Kenya da Algeria za su buga wasan karshe

Hakkin mallakar hoto google
Image caption Tawagar kwallon raga ta Volley ta matan Kenya

Kenya ta doke Senegal da ci uku da nema a wasan dab da kusa dana karshe da kungiyoyin biyu suka buga a gasar kwallon raga ta Volley ta mata da ake yi a birnin Nairobi, a Kenya.

A daya wasan kuwa Algeria mai kare kambun ta ne ta doke Masar da ci kuk da guda.

A yanzu haka dai kasashen biyu za su kara ne a wasan karshe a ranar laraba.

Najeriya dai wadda bata lashe wasa ko guda ba a gasar ta sha kashi a hannu Tunisia da ci uku da guda a wasan neman matsayi na biyar da na shida.

A yanzu haka dai Najeriyar za ta fafata ne Bostwana a ranar talata domin neman matsayin na bakwai ko na takwas a gasar.