'Yan wasa a Spain na ci gaba da yajin aiki

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasa tsakanin Barcelona da Real Madrid

'Yan wasa a Spaniya na ci gaba da yajin aiki, bayan kungiyarsu da jami'an shirya gasar sun kasa cimma yarjejeniya.

Bangarorin biyu dai basu cimma yarjejeniya ba a tattaunawar da su kayi a ranar litinin, abun da ke nuni da cewa akwai yiwuwar a kara samun jinkiri wajen fara gasar a wannan makon.

A makon daya gabata ne dai ya kamata a fara gasar, amma bai yiwu ba saboda hukumar shirya gasar da kuma 'yan wasan sun kasa cimma yarjejeniya.

Idan har ba'a fara kakar wasan bana ba a gasar ta Laliga a wannan makon, akwai yiwuwar sai ranar 10 ga watan Satumba, za'a fara saboda wasannin kasa da kasa da za'a buga a wannan zagon.