Uefa ta dakatar da Arsene Wenger wasanni biyu

Arsen Wenger Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Arsen Wenger yana cikin tsaka mai wuya a 'yan kwanakin nan

Hukumar kula da kwallon kafa ta Turai Uefa ta dakatar da kocin Arsenal Arsene Wenger wasanni biyu bayan da ya ki mutunta dakatarwar da aka yi masa a baya.

An kuma ci tarar Arsenal Euro 10,000 bayan da aka sami jami'ansu da halayyar da bata dace ba.

An dai yanke masa hukuncin ne bayan da aka same shi da laifin magana da 'yan wasansa duk da cewa an dakatar da shi daga wasan da Arsenal ta kara da Udinese ranar Talata, 16 ga watan Agusta.

Arsenal dai ta ce za ta daukaka kara kan hukuncin.

Hukuncin zai fara aiki nan take, inda Wenger ba zai shiga fili ba a zagaye na biyu na wasan share fagen shiga gasar cin kofin zakarun Turai da Arsenal za ta fafata da Udinese a Italiya.

Sanarwar da Uefa ta fitar ta ce: "Kwamitin da'a na Uefa ya dakatar da Arsene Wenger daga gudanar da ayyukansa a wasanni biyun da Arsenal za ta kara a gasar cin kofin zakarun Turai nan gaba".