Ferguson ya jinjinawa Welbeck

Image caption Danny Welbeck

Kocin Manchester United, Sir Alex Ferguson ya jinjinawa Danny Welbeck da sauran matasan kungiyar bayan sun doke Tottenham da ci uku da nema.

Welbeck, ne ya zura kwallon farko a wasan ana minti 61 a filin Old Trafford a ranar lintinin.

Dan wasan dai na cikin yan wasan goma shada daya da su ka buga wasan wanda suke kasa da shekaru 23.

"Danny nada shekaru 20 ne kawai, yana da kyakyawar makoma a kungiyar." In ji Ferguson.

Welbeck ya taka rawar gani sosai bayan an dawo hutun rabin lokaci a wasan.