Arsenal na zawarcin Eden Hazard

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Eden Hazard

Arsenal ne neman siyan dan wasan tsakiyan kungiyar Lille ta Faransa wato Eden Hazard.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 20, dan asalin kasar Belgium ne kuma ya kulla yarjejeniya da kungiyar Lille har zuwa shekara ta 2015.

Rahotannin dai na nuni da cewa dan wasan zai kai fam miliyan 26.

Arsenal dai na neman siyan Hazard ne domin maye gurbin Samir Nasri da kuma Cesc Fabregas.

Hazard ne dai ya lashe gwarzon dan wasan gasar Ligue 1 a Faransa a kakar wasan bara.