Hukumar kwallon Spaniya za ta binciki Mourinho

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana dai yawan hatsaniya idan ana wasa tsakanin Real Madrid da Barcelona

Hukumar kwallon Spaniya ta ce za ta binciki kocin Real Madrid, Jose Mourinho, saboda hatsaniyar da akayi a wasan Supercopa da kungiyar ta buga da Barcelona.

Ana zargin Mourinho ne da sanyawa mataimakin kocin Barca Tito Vilanova dan yatsa a ido a karshen wasan.

An dai sallami 'yan wasan Madrid Marcelo da Mezut Ozil da kuma dan wasan Barca David Villa, a wasan da Barca ta yi nasara da ci uku da biyu.

A wasan farko da kungiyoyin biyu su ka buga a gidan Madrid, sun tashi biyu da biyu ne.

Hukumar kwallon Spaniya dai ta dakatarda 'yan wasan uku gabaki daya.

Barcelona dai a ranar Litinin ta ce ba za kai karar Mourinho ba, amma dai Hukumar kwallon kafan Spaniya ta ce za ta bincike lamarin.