Fulham na zawarcin Demba Cisse

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Demba Cisse

Fulham ta shiga cikin sahun kungiyoyin dake neman siyan da kasar Senegal dake takawa Freiburg leda Papiss Demba Cisse.

Fulham na daga cikin kungiyoyin uku da ke zawarcin dan wasan mai shekaru 26 da haihuwa.

Ana dai ganin dan wasan zai kai fam miliyan goma sha uku.

A kakar wasan bara Cisse ya zura kwallaye 22 a gasar Bundesliga ta kasar Jamus.

"Ina son in koma wata kungiyar in dan taka leda." In ji Cisse