Kwallon gora: Ingila ta kai wasan kusa da na karshe

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Akwai yiwuwar Ingila ta hadu da Jamus

Tawagar mazan Ingila sun shiga rukunin matan kasar, inda ta tsallake zuwa zagayen wasan kusa dana karshe a gasar kwallon gora ta Turai.

Ingila dai ta lallasa Faransa ne da ci takwas da guda a wasan karshe da ta buga a rukunin da take kafin ta kai matakin kusa dana karshe.

Ashley Jackson ya zura kwallaye uku a wasan a yayinda Richard Alexander da kuma James Tindall, kowannensu ya zura kwallaye biyu.

Adam Dixon ne dai ya zura kwallon karshe.

Akwai yiwuwar Ingila ta buga da mai masaukin baki wato Jamus a wasan kusa dana karshe a ranar Juma'a.

Jamus dai ce ke jagorancin rukunin da take bayan ta lashe wasanni biyun da ta buga a gasar, kuma za ta kara ne da Rasha.