Holland ce ta daya a harkar tamoula

Kasar Holland ta maye gurbin Spaniya a matsayin na daya a harkar tamoula kamar yadda Hukumar kwallon kafa ta duniya wato Fifa ta fitar a watan Agusta.

Spaniya wadda ta lashe gasar kofin duniya dana Turai ta sauko kasa ne zuwa mataki na biyu bayan da ta sha kashio a hannun kasar Italiya a wasan sada zumunci.

Duk da cewa dai an dage wasan sada zumunci da Ingila za ta buga da Holland, kasar ta yunkuro sama saboda kashi da Brazil ta sha hannun Jamus.

Kasar Holland dai ta zama kasa ta bakwai da ta samu wannan karramawa na Fifa bayan kasashen,- Argentina da Brazil da Faransa da Jamus da kuma Italiya.

Jerin kasashen da Fifa ta fitar a watan Agusta

1 Holland

2 Spain

3 Jamus

4 Ingila

5 Uruguay

6 Brazil