Juan Mata ya koma Chelsea daga Valencia

Image caption Juan Mata

Juan Mata ya koma Chelsea daga kungiyar Valencia akan fam miliyan ashirin da uku da rabi.

Mata ya cimma yarjejeniya na tsawon shekaru biyar da Chelsea kuma zai takawa kungiyar leda a wasanta da Norwich a ranar lahadi.

"Valencia babbar kungiya ce, amma na bar ta ne domin in koma kungiyar da ta fita girma." In ji Mata mai shekarun haihuwa 23.

"Ina neman dama ce domin in lashe kofuna, kuma ina ganin ina da wannan damar a Chelsea."