Chelsea ta taya Alvaro Pereira daga Porto

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Alvaro Pereira ya iya kai hari sosai duk da cewa dan wasan baya ne

Kocin Chelsea, Andre Villas-Boas ya bayyana cewa kungiyar ta taya dan wasan bayan Porto Alvaro Pereira, amma ya ce bashi da kwarin gwiwa cewa kungiyar za ta sayi dan wasan.

Dan wasan mai shekarun haihuwa 25 ya buga karkashon Villas Boas a Porto, kuma ya taimakawa kasarshi ta Uruguay lashe gasar Copa America.

"Mun taya dan wasan, amma kudin da aka sa akansa ya yi yawa." In ji Villas-Boas.

Villas-Boas dai ya sayi wasu 'yan wasa masu tsada a kungiyar Chelsea tun da ya dauki ragamar jagorancin kungiyar.